Kaduna: Gabar Siyasa Na Kara Kamari A Tsakanin El-Rufai Da Uba Sani

IMG 20240331 WA0047

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmed El-Rufai, ya ce bai damu da yun?urin da majalisar dokokin jihar ke yi na bincikar gwamnatinsa ba.

El-Rufai ya yi nuni da cewa mai yiwuwa gwamnatin ba za ta yi nasara ba.

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana hakan a wani taron Sallah da ya yi da mu?arrabansa a ranar Talata 18 ga watan Yunin 2024.

El-Rufai ya kuma shawarce su da su guji yin cacar baki da hadiman gwamnan, inda ya yi hasashen cewa Uba Sani bayan ya gama ?an tsalle-tsallensa, zai fa?o kamar alewa a hannun yaro.

“Ku tallafawa gwamna da ?an majalisarsa da addu’o’i domin su yi abin da ya dace.” “Kada ku ji zafi kan abin da ke faruwa. Idan ya gama ?an tsalle-tsallen, zai fa?o kamar alewa (a hannun yaro).”

Wannan dai shi ne karon farko da tsohon gwamnan ya yi magana a bainar jama’a tun bayan da rikici ya ?arke tsakaninsa da magajinsa.

Related posts

Leave a Comment