Gwamnatin Tarayya ta sanar da amincewar sake komawa makarantu a ranar 18 ga Janairu bayan cimma yarjejeniya da Gwamnoni, Kwamishinoni da sauran masu ruwa da tsaki a harkar Ilimi da lafiya.
An cimma matsayar ne a wata ganawa tsakanin Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu da Kwamishinonin Ilimi a birnin tarayya Abuja.
Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Arc. Sonny Echono, wanda ya tabbatar da hakan ya ce: “Mun tattauna sosai tare da gwamnonin jihohi, masu makarantu, kungiyoyin kwadago da na ma’aikata da wakilan daliban.
Kuma yarjejeniya ita ce cewa ya kamata mu sake bu?e duk makarantu.
“Amma sake bude makarantun zai kasance cikin bin ka’idoji na COVID-19, musamman tsananin bin hanyoyin da ba magunguna.”
A wani labarin na daban Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce rufe makarantu saboda annobar COVID-19 zai yi tasiri mara kyau a kan ci gaba, aminci da kuma lafiyar yara a duniya, yana mai tabbatar da cewa makarantu ba hanyoyin cutar ba ne.
UNICEF ta kuma yi gargadin cewa sakamakon rufe makaranta har shekara guda za a ji shi har zuwa shekara mai zuwa. A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Talata ta ci gaba da cewa duk da kwararan shaidu da ke nuna cewa makarantu ba hanyoyi ne na cutar ba, an dauki matakai don tabbatar da cewa sun kasance a rufe.
