#EndSARS: Obasanjo Ya Yaba Jawabin Shugaban ?asa

Tsohon Shugaban ?asa Cif Olusegun Obasanjo ya yaba ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan jawabin kasa da yayi kan zanga-zangar EndSARS ranar Alhamis da ta gabata.

Tsohon Shugaban kasar ya kasance daya daga cikin shugabannin Najeriya da ke raye wadanda Buhari ya gayyata zuwa wani taro na yanar gizo a ranar Juma’a, 23 ga watan Oktoba.

Da yake magana a wajen taron, Obasanjo ya yaba ma Shugaban kasa Buhari a kan nunawa da yayi cewa zanga-zangar lumana na daga cikin damokradiyyar Najeriya.

Idan ba a manta ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya a yammacin ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoba, a yayinda ake tsaka da zanga-zangar neman shugabanci nagari da kawo karshen cin zalin ‘yan sanda.

A jawabin nasa, Shugaban kasar ya dakatar da zanga-zangar EndSARS sannan ya bayar da tabbacin cewa za a biya wa masu zanga-zangar bukatunsu. Daga bisani Buhari ya karbi bakuncin dukkanin tsoffin shugabannin Najeriya da suka hada da Goodluck Jonathan, Obasanjo da sauransu domin sanar da su halin da kasar ke ciki.

Da yake magana a taron, Obasanjo, wanda ya bayyana cewa “kasar na ta jira” ya ce ya yi farin ciki da ganin cewar an amshi bukatun masu zanga-zanga.
“Na yaba da jawabin daren jiya. Kasar na ta jira. Ka yi zantuka masu ma’ana da suka cancanci yabo.
“Zanga-zangar lumana na daga cikin koyarwar damokradiyya. An amshi bukatun masu zanga-zanga na hakika, kuma kana aiki a kan aiwatar da su. Mun jinjina maka.”

Related posts

Leave a Comment