CORONA Ta Kama ‘Yan Bautar ?asa 138

Rahotanni daga HukumarHukumar hana ya?uwar cututtuka a Najeriya NCDC ta bayyana cewar a?alla masu bautar kasa 138 ne suka kamu da cutar COVID-19.

Darekta janar na Hukumar ta NCDC Dr Chikwe Ihekweazu ne ya sanar da hakan, a lokacin da yana sanar da jami’an kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa a birnin tarayya Abuja.

A cewarsa, NCDC tana iyakar kokarin ganin ta karasa bude duk wasu sansanin masu bautar kasa da ke cikin kasar nan, ya ce wadanda suka harbu da cutar na daga cikin masu digiri 34,785 da kuma ma’aikatan sansanin da aka yi wa gwaji a makon da ya gabata ne.

Ya ce hakan yana nuna kashi 0.4 ne ke dauke da cutar wanda a kalla ana iya samun mutum daya a cikin kowanne Mutum 200 kenan inji shi.

Ya kara da jaddada cewa an samu manyan nasarori wurin bude sansanin ‘yan bautan kasa kuma ba a ba ko mutum daya mai dauke da cutar damar shiga sansanin ba.

“Wadanda aka tabbatar suna dauke da cutar ana musu magani daga gida ne ko kuma cibiyar killacewa, hakan ya dogara da yanayin karfin cutar a jikinsu,” inji shi.

Related posts

Leave a Comment