Bauchi: Rera Wa?ar Coci Da Sarki Ya Yi Ta Tada ?ura

Wani hoton bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta ya janyo hankulan ‘yan Najeriya musamman masu amfani da Twitter. A cikin bidiyon, An gano Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Suleiman Adamu, yana rere wakokin yabo na addinin kirista tare da ‘matan zumunta’ a yayin da suka kai masa ziyara fadarsa.

Kungiyar Matan Zumunta fitaciyyar kungiya ce ta masu waka a Kiristocin arewacin Najeriya da aka san su da iya rere wakokin addinin kirista masu ratsa zuciya.

Dakta Adamu shine sarki na 11 a masarautar Bauchi kuma sarki mai ci a yanzu. Ya yi karatun digirin farko a Fasahar Gini daga Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Wasu da dama sun yaba wa abinda sarkin ya yi inda suka ce hakan na iya hada kan al’ummar jihar da kasa baki daya, yayin da wasu kuma jama’ar ke sukan hakan suna ganin ya ci karo da tsarin Masarautar Bauchi da aka gina akan tsarin tafarkin Islama.

A karshen makon da ya gabata ne kungiyar Matan Kiristocin ta kai ziyara fadar Sarkin na Bauchi, a wani bangare na sadar da zumunta da kuma girmamawa ga Masarautar ta Bauchi mai tsohon tarihi.

Jihar Bauchi da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya jiha ce wadda ta tara dimbin jama’a da ?abilu mabanbanta masu bin addinai daban-daban.

Related posts

Leave a Comment