Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi ya gabatar da kasafin kudi kimanin naira biliyan 213 na shekarar mai kamawa ta 2021 a majalisar dokokin Jihar.
Gwamnan yace harsashen kasafin kudin na bana ya dara na bara da naira biliyan 46, inda yace sunyi mashi lakabi da suna cikamakoken kasafin kudin jihar na 2021.
Bala ya gayama yan’majalisar cewa anyi kiyasin kasafin ne tare da kididdigan harsashen 213,914,559.428 wanda ake sa ran manyan ayyuka zasu lakume naira 120,717,251,458 kashi 56 na kasafin, a yayin da naira 93,197,307,970 kashi 44 zai tafi zuwa ga ayyukan yau da kullun.
Gwamnan y’all kara da cewa kasafin kudin an shiya shine akan la akari da harsashen farashin danye mai na kasa da kuma sauyin farashin chanji na kudi da kuma harsashen kudin shiga damn ake karba na haraji.
Inda ya kuka da cewa harsashen kasafin kudin ya ci karo da matsaloli na aiwatarwa damn kasafi shekara mai shudewa tare da cutar annobar mashakon numfashi da ya kassara tattalin arzikin kasa da na duniya baki daya.
Anashi tsokacin lokacin gabatar da kasafin kudin kakakin Majalisar Jihar Bauchin Abubakar Y. Sulaiman, yace zasu bama bangaren zartawa dukkan wani goyon baya don ganin kasafin kudin ya cimma burinsa na samarda ayyukan ci gaba da more rayuwar talakan jihar.
Kana Kakakin, ya kara da cewa su a majalisar dokokin jihar, yayin da sukashigo kwaryar majalisa to aikin al’ummar jihar Bauchi suke sawa a gaba, duk da bambamce-bambamce dake tsakanin su na siyasa ko jam’iyya.
Daga karshe yace zasu gudanar da muhawarar a tsakanin su yan’majalisar da zarar sun shiga zama don samun zarafin bangaren zartawa don rattaba hannu akan kasafin ya kuma zama doka nan take.
Daga Adamu Shehu Bauchi
