?aya daga cikin ?ungiyoyin Fulani makiyaya a Najeriya, Miyetti Allah Kautal Hore ta bu?aci hukumomin tsaron kasar su hukunta ?an bindigar da ke kashe Fulani makiyaya a yankin Kudu maso Gabashin kasar.
Mai magana da yawun ?ungiyar Saleh Alhassan cikin tattaunawar da ya yi da jaridar The Punch, ya bayyana haka a matsayin martani ga kisan ?aya daga cikin kwamandojin haramtacciyar ?ungiyar IPOB mai fafutukar kafa ?asar Biafra da jami’an tsaro suka yi ranar Asabar.
Tun farko jaridar ta rawaito yan sanda da takwarorinsu sojoji da jami’an hukumar farin kaya sun halaka jagoran IPOB mai suna Ikonso da wasu mutum shida a jihar Imo.
Sai dai mai magana da yawun kungiyar Miyetti Allah ya yaba wa jami’an tsaro inda “ya nemi su ?ara azama wajen murkushe duk wasu masu tada zaune tsaye a Najeriya”.
Ya ce kimanin Fulani 50 aka kashe a Kudu maso Gabashin kasar cikin wata daya da ya gabata.
