Rahotanni daga yankin ?aramar Hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna na bayyana cewar Hukumar za?e mai zaman kanta, INEC, ta bayyana Alhaji Usman Baba na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe za?en cike gurbin ?an majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakilta maza?ar Sabon Gari.
Baturen za?en yankin mai suna Malam Mohammed-Nuruddin Musa, shine ya fa?i sakamakon za?en ranar Asabar a sakatariyar ?aramar Hukumar dake Zaria.
Yace Baba na jam’iiyar PDP ya lashe za?en da ?uri’u 9,113, yayin da ya kayar da babban abokin gwabzawarsa, Malam Musa Musa, na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 7, 404.
Baturen za?en yace: “Alhaji Usman Baba na jam’iyyar PDP, shine ya lashe za?en cike gurbi na ?an maja?isar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Sabon Gari.” Dr. Musa ya ?ara da cewa, Malam Anas Abdullahi, na jam’iyyar ADC ya samu ?uri’u 62; Chindo Ibrahim, na jam’iyyar ADP ya samu kuri’u 61, yayin da Musa Halilu na PRP ya samu ?uri’u 304.
