Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da ma’aikatan hukumar fansho ta makarantar firamare a kan zarginsu da ake da waskar da kudi har N553.985,644.1.
Kudin an adana shi ne domin biyan malaman makaranta da suka yi ritaya kudin sallama da na fansho, inda Jami’an suka yi nasarar waskewa dasu.
Ma’aikatan sun hada da: Abubakar Aliyu, Hassana Moyi, Haliru Ahmad, Kabiru Ahmad da Dahiru Muhammad Isa.
An gurfanar da jami’an a gaban wata babbar kotu a Sokoto a kan laifuka 28 da suka hada da cin amana da almundahana wanda suka ci karo da sashi na 92, sakin layi na biyu na dokokin Penal Code.
A yayin bayani, shugaban EFCC na yankin, Usman Bawa Kaltungo, ya ce ma’aikatan sun yi amfani da sa hannun bogi inda suka cire kudin sallamar malamai da na fansho a jihar.
Yadda aka cire kudin Kaltungo wanda yace yayi aiki ne kan korafin da daya daga cikin masu fanshon ya kawo masu, ya ce tsakanin 17 na watan Janairun 2017 zuwa watan Maris na 2020, daraktan kudin ya cire kudi da ya kai miliyan 83.2 daga asusunsu na banki.
“A wannan lokacin, Halliru da Kabiru sun cire 203,217,770.71 da 266,567,053 daga asusun bankin da sunan ‘yan fanshon,”. “Da kanmu muka biya kudin motan wasu daga cikin ‘yan fanshon domin su zo bada shaida, sun matukar girgiza ganin cewa kudaden da suka dade suna tarawa aka waskar.”
