Hajjin Bana: Mazauna Saudiyya Ne Ka?ai Za Su Sauke Farali

Hukumomi a Saudiyya sun ce jumillar mutum 60,000 ne kacal aka yarda su gudanar da aikin Hajji na bana, a cewar shafin Haramain Sharifain mai bayar da bayanai daga masallatan Harami biyu.

Kazalika, mazauna Saudiyya ne ka?ai za su gudanar da aikin na shekarar Hijira ta 1442, wa?anda suka ?unshi ‘yan ?asa da kuma ba?i.

Shafin ya ce an ?auki matakin ne sakamakon ya?uwar sababbin nau’uin cutar ta korona a ?asashen duniya.

Haka nan, rukunin mahajjata guda uku ne ka?ai za a bai wa damar yin ibadar. Su ne:

  • Wanda aka yi wa rigakafin korona
  • Wanda aka yi wa rigakafi guda ?aya kuma ya shafe kwana 14
  • Wanda aka yi wa rigakafi amma bai gama warkewa ba

?ullar cutar korona a fa?in duniya ta sa dole an sauya yadda ake gudanar da abubuwa da dama na yau da kullum ciki kuwa har da ayyukan ibada – kamar sallah cikin jam’i da daidaita sahu a sallar da ma yadda ake ayyukan Hajji da Umra kamar shi ?awafin da safa da marwa da dai sauransu.

Da yake ?awafi na ?aya daga cikin manyan ayyukan Umrah da Hajji, hukumomin Saudiyya sun samar da hanyoyin yin sa yadda ba za a sa?a dokokin cutar korona ba.

A yanzu an sanya alama a ?asan filin ?awafi don nuna wa masu ?awafi yawan tazarar da ya kamata su bari a tsakaninsu.

Kamar yadda aka saba dama, akwai ?an sanda ko jami’an masallaci da ke shawagi a filin ?awafi tun kafin zuwan cutar korona amma a masallacin Ka’aba yanzu, akwai jami’an masallaci na musamman da ke sa ido domin tabbatar da cewa maniyyata sun bar tazarar da ya kamata wato ba su cunkushe a wuri guda kamar yadda aka sani ba.

Dama kuma akwai iya adadin mutane da ake bari su shiga masallacin a lokaci guda ta hanyar amfani da wata manhaja don haka zai yi wuya a samu cunkoson mutane.

Sannan duk da tazarar da ake bari, dole ne mai yin ?awafi ya sanya takunkumin fuska har ya fita daga masallaci.

Haka kuma, ba kamar yadda aka saba ba yanzu masu sanye da Ihrami ne kawai ake bari su shiga filin ?awafi, amma su ma ba a bari su je kusa da Ka’aba.

An kewaye Ka’abar da wasu robobi da za su hana mutane wucewa su je kusa da ita.

Don haka babu ta?a Ka’aba da Hajrul Aswad da tsayuwa a ?ar?ashin indararon rahama kamar yadda aka saba.

Related posts

Leave a Comment