Bauchi: Gwamna Bala Ya Rushe Majalisar Zartarwar Jihar

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed Abdulkadir ya sauke Sakataren Gwamnati da Shugaban ma’aikatan gidan Gwamnati tare da sauran dukkanin Yan’majalisun zartarwar Jihar tare da masu bashi shawara nan take

Sanarwar ta fito ne da sanyin safiyar laranan nan tare da sa hannun mai ba Gwamnan shawara kan harkokin watsa labarai Comrade Mukhtar Gidado, takardar ta kara da cewa dukkan masu role da mukamai na siyasa suma su ajiye aikinsu nan take ba tare da Mata lokaci ba

Haka nan Sanarwar tayi nuni da cewa mai bada shawara kan harkokin tsaro, da mai bada shawara kan yan’majalisu da Mai bada shawara kan harkokin Shirin tallafi Gwamnati tarayya na matasa (Social Investment Program) sai mai bada shawara kan harkokin watsa labarai, zasu ci gaba da rike mukamansu.

Har’ila yau Sanarwar ta kara da cewa “dukkanin kwamishinoni su mika ragamar ma’aikatunsu ga manyan sakatarotin su nan take, kana shima sakataren Gwamnati da Shugaban ma’aikatan gwamnatin da su mika ragamar ofishinsu ga wanda ya fi kowa matsayi a nasu bangaren wadanda zasu gudanar da binciken kan kayayyakin gwamnati” Sanarwar ta tabbatar.

Gwamnan Bala ya godewa Yan’majalisar da abun ya shafa, da Kuma basu kwarin gwiwa da addu’ar Allah ya taimakesu a kan abunda zasu samu nan gaba a rayuwarsu. #

Related posts

Leave a Comment