Kamfanonin Sadarwa Sun Dakile Hanyar Shiga Shafin Tiwita A Najeriya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kamfanonin sadarwa a Najeriya kamar MTN, Glo, Airtel da 9mobile sun fara rufe amfani da damar shiga dandalin sada zumunta twitter, domin biyayya ga umarnin gwamnatin tarayya na dakatar da amfani da shafin Tiwita a Najeriya.

Kamfanonin sun ce sun samu sa?on umarni daga hukumar sadarwa ta ?asa NCC cewa su tsayar da damar shiga twitter a ?asa biyo bayan umarnin gwamnatin tarayya na dakatar da shafin.

‘Yan Najeriya masu amfani da twitter sun wayi garin ranar Asabar ba tare da samun damar amfani da shafinsu na twitter ba, yayin da wasu ke amfani da wata manhajar sadarwa domin shiga shafin su.

Kamfanonin sadarwar Najeriya baki ?aya sun bayyana ?ar?ashin ?ungiyar su cewa sun fara dakatar da damar amfani da twitter a wani jawabi da suka fitar ranar Asabar.

Jawabin wanda a ka yiwa take da “Umarnin dakatar da amfani da twitter a Najeriya” wanda shugaban ALTON, Gbenga Adebayo, da sakatarensa, Gbolahan Awonuga, suka sanya wa hannu.

Wani sashin jawabin yace: “Mu, ?ungiyar kamfanonin sadarwa ALTON, mun tabbatar da mambobin mu sun samu umarni daga NCC cewa su dakatar da bayar da damar amfani da twitter.” “Mambobin mu sun yi biyayya ga umarnin da hukumar sadarwa NCC ta basu, kuma zasu cigaba da biyayya ga dukkan umarnin da hukumomi da masu fa?a aji suka basu a Najeriya.”

Related posts

Leave a Comment