An Yi Allah Wadai Da Yunkurin Halasta Shan Tabar Iblis A Najeriya

Shugaban hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi, NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya) ya yi gargadin cewa yunkurin da wasu ke yi na ganin an halasta amfani da Tabar Iblis wato wiwi a Najeriya zai janyo wa kasar koma baya a nasarar da ta samu wurin yaki da sha da safarar muggan kwayoyi.

Marwa ya yi wannan gargadin ne yayin jawabinsa wurin taron tsaro da majalisar wakilai ta kasa ta shirya a ranar Laraba a zauren Majalisar dake babban birnin tarayya Abuja.

A cewarsa, akwai kwakwarar alaka tsakanin shan miyagun kwayoyi da kallubalen tsaro a kasar. “A halin yanzu babu abin da ya fi ciwa Najeriya tuwo a kwarya kamar matsalar tsaro.

Tabar Iblis na daga cikin manyan kallubale idan ma ba ita bane mafi girma. Rashin tsaro babban matsala ne a yau da ta haifar da wasu matsaloli kamar tada kayan baya, yan bindiga, garkuwa da mutane, kisa, fashi, kisar ramuwar gayya da sauransu,”.

Ya cigaba da cewa akwai kwakwarar alaka tsakanin shan miyagun kwayoyi da aikata laifuka, ana iya gani karara cewa babu yadda dan adam zai tashi yana aikata irin manyan laifukan da ake yi a kasar nan a baya bayan nan idan ba tun farko ya kausasa zuciyarsa da muggan kwayoyi ba. Marwa ya kuma ce alkalluma da bayanai da aka tattara sun nuna cewa amfani da haramtattun kwayoyi na bada gudunmawa wurin tabarbarewar tsaro.

Related posts

Leave a Comment