Uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Babban hafsan sojan Najeriya Janar Ibrahim Attahiru.
Aisha Buhari ta wallafa hotunan ziyarar ta’aziyar a shafinta na Twitter tare da sa?on ta’aziyya.
A ranar Asabar aka binne Babban Hafsan sojan tare da sojoji 10 da suka mutu a hatsarin jirgin sama a Kaduna.
Aisha Buhari ta ce rasuwar babban hafsan sojin babban rashi ne ga iyalansa da kuma Najeriya baki ?aya.
