Da ?umi-?umi: ‘Yan Bindiga Sun Bindige ?an Sarkin Kwantagora

Rahotanni daga Masarautar Kwantagora dake Jihar Neja na bayyana cewar ?an Sarkin Kontagora, Alhaji Bashar Saidu Namaska, na cikin mutanen da ‘yan bindiga suka hallaka yayinda suka kai hari gonar Sarkin a ranar Laraba, 19 ga Mayu, 2021.

An ruwaito cewa ‘dan Sarkin na tare da wasu mutane ne cikin gona dake titin Zuru Kwantagora lokacin da ‘yan bindiga suka kai musu farmaki.

‘Yan bindigan sun yi awon gaba da shanu da dama. Majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun tare matafiya a hanyar fashi da makami inda suka kwace wayoyi, kudade da wasu kayayyaki hannunsu.

A cewar majiyoyin, an lallasa duk wanda bai da kudi ko dukiya kuma akayi awon gaba da su cikin daji.

‘Dan sarkin wanda shine Sardaunan Kontagora ya kasance mai taya mahaifinsa Sarkin Sudan, Alhaji Saidu Namaska, abubuwa tunda ya fara rashin lafiya.

Related posts

Leave a Comment