Za Mu Taimaka Wajen Ganin Abubuwa Sun Daidaita A Chadi – Buhari

Shugaba Buhari ya fa?a wa Janar Mahamat cewa Najeriya za ta tallafa wajen daidaita Chadi da kuma tabbatar da komawarta kan tsarin mulkin dimokura?iyya.

“Najeriya ta san irin rawar da Chadi ta taka wajen taimaka mata a ya?i da ta’addanci kuma muna godiya sannan za mu ci gaba da wannan ala?ar”, in ji Buhari.

“Nahiya da al’adu sun ha?a ?asashenmu waje guda, saboda haka za mu taimaka a cikin duk abin da za mu iya”.

Buhari ya kuma bayyana mahaifin sabon shugaban Chadin wato Idris Deby Itno a matsayin abokinsa kuma abokin Najeriya.

?asashen Chadi da Najeriya da Nijar da Kamaru na cikin hukumar kula da Tafkin Chadi mai suna Lake Chad Basin Commission (LCBC), wadda aka kafa don kula da kuma ha?aka shi.

Buhari ya tabbatar wa da takwaran nasa cewa Najeriya za ta ci gaba da ayyukanta a ?ungiyar tsaron ha?in gwiwa tsakanin ?asashen ta MNJTF.

A jawabinsa, Janar Mahamat Idriss Deby ya gode wa Najeriya bisa irin goyon bayan da aka nuna musu bayan mutuwar mahaifinsa kuma tsohon shugaban Chadi.

“Kana cikin na kusa-kusa ga Marshal Itno. Na zo ne domin na ?arfafa wannan ala?ar da kuma neman ka taimaka mana wajen shugabancinmu.

“Mun dogara a kan ‘yar uwarmu Najeriya kamar yadda muka ha?a al’ada da nahiya. A shirye muke mu yi amfani da taimakonka don komawa kan tsarin dimokura?iyya.”

Ya kuma sake nanata kudirinsa na ganin an gudanar da sahihin za?e nan da wata 18.

Related posts

Leave a Comment