Majalisar ?inkin Duniya Ta Nemi A Saki Wanda Ya Yi ?atanci Ga Annabi

Wani kwamitin ?wararru na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga hukumomin Najeriya da su saki Mubarak Bala shugaban wadanda babu ruwansu da addini a Najeriya da ake tsare da shi tsawon shekara ?aya.

An tsare Mubarak Bala ne bayan shigar da koke ga‘yan sandan jihar Kano a arewacin kasar, kan zargin ya ci mutuncin manzon Allah a wani rubutu da ya yi a Facebook.

?wararrun na Majalisar ?inkin Duniya sun ce “Kamewa da tsarewar da aka yi wa Mista Bala ba wai kawai take ha??in dan adam ba ne, ya yi tasiri a kan aiwatar da ?ancin walwala a Najeriya.”

Sun ce sun yi takaicin yadda hukumomi suka ki bin umarnin da Babbar Kotun Tarayya ta bayar a 21 ga Disamba na sakin Mista Bala.

Kotun ta bu?aci a bayar da belinsa da kuma biyansa ku?i 250,000 kan keta ha??insa.

A ranar 20 ga Afrilu aka shirya sauraren ?arar amma aka ?age saboda yajin aikin ma’aikatan shari’a.

Kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da cewa an mutunta dokokin shari’a.

Related posts

Leave a Comment