Wasu da ake zargi ?an kungiyar masu neman kafa kasar Biafra, IPOB, sun yi wa makiyaya fulani 19 yankan rago a Igbariam da ke ?aramar hukumar Oyi ta jihar Anambra. Rahotanni sun ce ?an daban sun afka wani bene da makiyaya fulanin ke zama ne misalin ?arfe 2 na daren ranar Asabar.
?ata garin sun halaka mata 12, maza bakwai da ?ananan yara da ba a san addinsu ba. An gano cewa bata garin sun fito da wadanda abin ya faru waje, suka cire musu tufafi suka ?auresu sannan suka yanka su.
Majiyarmu ta ruwaito cewa wakilinta ya samu hotuna marasa kyawun gani na gawarwakin wadanda abin ya shafa.
Wani mazaunin garin da ya nemi a boye sunansa ya ce bata garin sun datse kan maza uku, suka yanke al’ura da wasu sassan jikin matan suka tafi da su.
Majiyar ta ?ara da cewa bata garin sun kashe shanu 25, sun raunata 19 sannan suka yanka wasu guda biyar. “Yara biyu suna asibiti a halin yanzu. ?ata garin sun yi wa wani yaro ?an wata tara rauni a goshinsa. “
“Abin bakin cikin shine dukkan wadanda abin ya faru da su ?an uwa ne,” in ji majiyar. Kakakin rundunar yan sandan jihar Anambra, Ikenga Tochikwu bai amsa kira da aka yi masa ba har zuwa lokacin ha?a wannan rahoton.
