Kisan ‘Yan Arewa: Shiru A Arewa Ba Tsoro Bane – Babba Kaita

Sanata Ahmad mai wakiltar maza?ar Katsina ta Arewa a majalisar Dattawa Sanata Ahmed Babba Kaita, ya yi kira da babbar murya akan a dakatar da kashe ‘yan arewa da ake faman yi a kudancin ?asar nan cikin gaggawa, ba tare da ?ata lokaci ba.

Sanata Babba Kaita, ya cigaba da cewar, kamar dai yadda yan kudancin ?asar nan ke walwala a Arewa, yakamta abar kowane ?an arewa ya yi rayuwa cikin kwanciyar hankali a sashin Kudancin kuma yakamata abarsu su yi kasuwancin a kudanci kamar yadda kundin tsarin mulkin ?asar nan ya tanada.

Idan zaku iya tunawa, kwanakin baya, gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya garga?i ‘yan kudancin ?asar nan dake rayuwa a arewa da kada su yi tsammanin kariya matu?ar aka cigaba da kashe ‘yan arewa a kudu.

Sanata Babba Kaita a wani ta?aitaccen jawabi da ya yi mai take ‘Arewa: babu sauran yin shiru’ ya ce a yanzun babban laifin ka shine ka zama ?an arewa. Ba zamu zuba ido muna Kallo ana kashe mana Mutane a Kudu ba.

“Dan kogi ya tsaya cak, bashi ke tabbatar da cewa babu Kadoji a ?ar?ashinsa ba, kamar haka ne don ana cin mutuncin arewa ta hanyoyi da dama kuma mun yi shiru, hakan ba yana nufin ‘yan arewa ba su iya ramuwar gayya bane ko kuma basu san yadda ake buga wasan ba.”

Sanatan wanda yana goyon bayan kujerar shugaban ?asa ta koma kudu a za?en 2023 ya ce ‘yan arewa sun yi shiru ne don kawai Najeriya ta cigaba da zama ?asa ?aya. Amma Kaita yace kowa ya yi da kyau to fa nan gaba shima zaiga dakyau, babu mai tantama akan wannan.

Ya ?ara da cewa a ko ina a fa?in duniya, gina ?asa ba aikin mutum ?aya bane, dole sai kowa ya bada ha?in kai, kuma Najeriya wani ?angare ne na duniya.

Related posts

Leave a Comment