Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ya dace a saka dokar da za ta hana kai shanu daga arewa zuwa kudu, domin da?ile rikicin da ya ?i ci ya ?i cinyewa tsakanin Manoma da Makiyaya a ?asar.
A yayin zantawa da manema labarai bayan haduwarsa da gwamnonin APC tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura, jihar Katsina, Ganduje ya ce idan har ba a hana yawon shanu ba, babu ranar kawo karshen rikicin manoma da makiyaya.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta shirya samar da wurin zama ga makiyayan a dajin da ke tsakanin iyakar Kano da Katsina, domin shawo kan matsalar.
Ya ce matsugunin zai kasance da gidaje, tafki, cibiyar dabbobi ta zamani da asibitocin dabbobi.
“Zamu gina matsugunin a dajn Samsosua, iyakarmu da Katsina kuma mun yi nasarar shawo kan illar ‘yan bindiga a yankin,”
“Za mu gina gidaje, tafkuna, cibiyar dabbobi, asibitin dabbobi kuma tuni muka fara ginawa makiyayan gidaje.
“Ina kira a kan a yi watsi da kaiwa da kawowa ko kuma yawon makiyaya daga sassan arewa zuwa tsakiyar kasar nan ko kudancin Najeriya.
“A saka dokar haramcin hakan ko kuma ba za mu iya shawo kan rikici tsakanin makiyaya da manoma ba kuma ba za mu iya hana satar shanu ba da ya addabe mu.”
