Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya canza dogarinsa mai kula da tsaronshi wanda akafi sani da ADC, kuma ya zabi sabon Dogarin da zai cigaba da kula da tsaronshi nan take.
Fadar Shugaban kasa ta sanar da cewa Laftanan Kanal Y. M Dodo zai maye Kanal Muhammed Abubakar, wanda ya ke matsayin Dogarin Buhari tun 2015.
A cewar majiyoyin, Kanal Abubakar zai ajiye aikinsa ne saboda halartan wani kwas domin ya samu karin girma zuwa matsayin Birgediya Janar.
Laftanan Kanal Dodo ya kasance hadimi ga kwamandan makarantar Sojoji NDA dake Kaduna.
Yanzu haka shugaba Buhari na mahaifarshi birnin Daura Jihar Katsina domin musharaka a shirin sabunta rijistan kasancewa mamba jam’iyyar.
