Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa gamayyar jami’an tsaro sun kutsa cikin gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda suka kwashe duka almajiran da ke kwance a tsakar gidan.
Shugaban makarantun Dahiru Bauchi na Kaduna da kewaye kuma limamin masallacin bye pass na Kaduna, Fatahu Umar Pandogari, ya tabbatar wa BBC da faruwar wannan lamarin.
“Da misalin 12:00 na dare Sojoji da ?an sanda da Kastelea da Road Safety suka shigo gidan Maulanmu Shehu, nan makaranta, suka kama almajirai suka tafi da su cikin daren,” in ji shugaban makarantar.
Ya bayyana cewa bai san dalilin da ya sa aka kama almajiran ba, amma tun bayan rufe makarantu lokacin ?ullar korona a karon farko, tun lokacin aka sallami ?aliban makarantar, amma a cewarsa, wa?anda aka kama a yanzu wa?anda suke zaune a gidan Sheikh Dahiru ne ba wai wa?anda suka taso suka zo daga wani gari ba.
“Ba za mu iya tantance ko almajirai nawa aka ?iba ba, domin cikin dare aka zo aka kwashe su,” in ji shi.
Ya kuma bayyana mana cewa sun yi ?o?arin tuntu?ar gwamnatin Kaduna a lokacin da abin ya faru, amma ba su samu damar magana da su ba.
Amma ko da BBC ta tuntu?i gwamnatin Kaduna, mai taimaka wa gwamnan Kaduna kan kafafen ya?a labarai Abdallah Yunus Abdallah, ya shaida mana cewa a halin yanzu ba za su ce komai kan wannan lamari ba, amma nan gaba ka?an za su fito su yi ?arin bayani.
Babu wani tabbaci dai kan dalilin da ya sa aka kai wannan samamen, amma ko a kwanakin baya sai da gwamnatin jihar ta ?wace lasisin wata makaranta da kuma rufe ta sakamakon zarginta da sa?a dokokin korona.
