Wasu ‘yanbindiga sun kai hari a kauyen Katarma da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka kashe mutum hudu ciki har da ‘yan banga tare da sace wasu mata.
Wani rahoton tsaro ya nuna cewa da fari ‘yan bindigar sun yi artabu da ‘yan bangar kauyen kafin daga bisani dakarun tsaro su kawo masu dauki.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, yana mai cewa jami’an tsaro sun yi nasarar ceto matan da aka sace.
A cewarsa, cikin gaggawa aka shirya mayakan sama a kauyen Katarma da Kasasu da ke kan iyaka da jihar Neja, don fatattakar ‘yan binidgar a ranar Laraba.
Lamarin ta?ar?arewar tsaro a jihar Kaduna na ?ara shiga cikin wani hali a har kullum, duk da bugun kirjin da gwamnatin jihar karkashin Nasiru El Rufa’i ke yi na samun galaba akan ‘yan ta’addan.
