Gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamar da shirin ‘yan sandan jiha a kokarinta na kawo karshen matsalar tsaro a fadin jihar. An yaye kwanstabul 272 daga makarantar bada horo a zango na farkon shirin.
Da yake jawabi ga sabbin ‘yan sandan jihar, Gwamna Nasir El-Rufa’i ya bayyana tsarin ‘yan sandan a matsayin abu mai matukar amfani/musamman idan akayi la’akari da shakakin tsaron da ake fuskanta.
Gwamnan da ya samu wakilcin kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida, Samuel Aruwan ya bukaci ‘yan sandan da su karfafa tsaro a fadin jihar.
Ya ce an zabo jami’an 272 daga kananan hukumomi 16 dake cikin jihar a matsayin kason farko, yayin da za a sake zabowa daga sauran kananan hukumomi 23 a kashi na biyu don inganta tsaron cikin gidan jihar.
Tun da fari, Kwamishinan ‘yansanda na jihar, Umar Muri ya shaida cewa bikin yaye ‘yan sandan na daga cikin tsare-tsaren hannanta jami’an a hannun gwamnatin jihar kafin tura kowanensu inda zai kama aiki.
