A Ceto ‘Yata Kamar Yadda Aka Ceto ?aliban ?an?ara – Mahaifin Leah Sharibu

Mahaifin Leah Sharibu Mista Nathan Sharibu ya fito fili ya koka dangane da cigaba da rike diyarshi Leah Sharibu tsawon lokaci da kungiyar Boko Haram ta yi, inda ya yi kiran da a gaggauta sakin diyar tashi kamar yadda aka sako ‘yan makarantar Kankara daga hannun ‘yan ta’adda.

Leah Sharibu na ‘yar shekara 14 lokacin da yan ta’addan Boko Haram suka saceta ranar 19 ga Febrairu, 2018, tare da kawayenta 110 a makarantarsu, GGSS Dapci dake karamar hukumar Yunusari ta jihar Yobe.

Tun daga lokacin ta kasance a hannunsu saboda ta ki amincewa ta canza addininta. Mahaifinta, Nathan, wanda yayi magana da manema labarai ranar Talata, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta taimaka ta ceto diyarsa bayan shekaru uku hannun yan ta’addan.

“Muna sake roko, muna rokon hukumomi su taimaka su ceto diyata. Na yi imanin zai yiwu saboda kwanan nan aka ceto dalibai a jihar Katsina,” inji mista Nathan

“An bar mu cikin bakin ciki na tsawon shekaru uku yanzu, tun lokacin da aka sace Leah. Na san gwamnati sun yi mana alkawura da yawa amma har yanzu diyata na cikin daji.”

“Wannan shine Kirismetinta na uku tun lokacin da aka saceta a Dapchi, amma muna sa rai.” A ceto min diyata kaman yadda aka ceto daliban Kanaka, inji mahaifin Leah.

Related posts

Leave a Comment