Ma’aikaciyar ya?a labarai ta gidan Talabijin da Rediyo na Liberty dake Kano Khadijah Ishaq Bawa ta lashe lambar girmawa ta aikin jarida na Jami’ar koyar da aikin jarida na Pan Atlantic.
Khadijah Bawa ta lashe lambar yabon ne ta la’akari da gogewarta wajen kawo rahotanni da suka shafi cigaban al’umma baki ?aya.
Bikin bada lambar yabon wanda ya gudana a ranar Lahadi a Lekki Legas, ya kuma bada wasu lambobin girmamawan ga wasu zakakuran ‘yan Jarida wadanda suka jajirce wajen kawo muhimman rahotanni da sharhi da ma?aloli daban daban.
Da take mayar da jawabi bayan karbar lambar girmamawar Khadijah Bawa ta gode wa shugabanni da abokanan aikin ta wadanda ta samu nasara dalilin aikin da su musanman abokin aiki MD Lawal, tare da yin alkawarin cigaba da gudanar da ayyukan ta yadda suka kamata.
Tun farko da yake jawabi shugaban shirye shiryen na makarantar Mr Isaac Ezechukwu yace babbar hikimar shirya wannan gagarumin taron shine domin zakulo ‘yan jarida wa?anda suka sadaukar da rayukan su wajen taimakon jama’a da wayar da kan al’umma.
