Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sani Khalil Rigasa

Rahotannin dake shigo mana yanzu na nuna cewa yan ta’addan da sukai garkuwa dashi sun harbeshi ne cikin daren alhamis.

Dama yan bindigar sun yi garkuwa da Sani Khalil makonni biyu da suka gabata bayan sun harbe Rabiu Auwal da Umar wanda hakan yai sanadiyar mutuwar Rabiu shi kuma Umar yana amsar magani a asibitin 44 dake Kaduna.

Daya daga cikin wanda suka biya kudin fansar ya shaida mana cewa masu garkuwa da mutanen sun shirya sako mutane biyar da sukai garkuwa dasu cikin daren alhamis bayan kammala yarjejeniya.

Masu garkuwa da mutanen sun harhada iyalan wanda sukai garkuwa dasu a zariya. Inda suka gayawa iyalan su hadu a zariya daga bisani suka sasu suka hau mota suka shiga galadimawa, inda daga nan suka ce a hau mashin a shigo dajin

Bayan sun bada kudi sun kammala komai sai aka fito da mutane hudu daga cikin wanda akai garkuwan dasu babu Sani Khalil.

Anan ne suka shaidawa wakilan Sani Khalil cewa saida aka fito dasu dukansu a hanya kawai suka harbe Sani Khalil sukace a ajiyeshi a kan wani yashi. Su gayawa yan uwansa suxo su dauke shi a nan. Yanzu haka dai iyalan marigayin sun masa salatul Gaib sakamakon zuwa dauko gawar nada hatsari da kuma rashin sanin takaimanmen inda za aga gawar tashi.

Allah ya jikan Sani Khalil Adam Rigasa kuma Allah ya raya zuri’ar da ya bari guda 5

Related posts

Leave a Comment