Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Manoma Yankan Rago

‘Yan ta’addan sun yi wa manoma har guda bakwai yankan rago har lahira a cikin karamar hukumar Sabuwar jihar Katsina.

Dan Majalissar dokokin jihar Katsina mai wakiltar mazabar Sabuwa Hon Ibrahim Kaka Machika shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a zauren majalissar a jiya Litinin.

Dan Majalissar ya ce daga cikin wadanda yan bindigar suka yanka har da wata uwa mai shayarwa.

Lamarin ya afku ne a kauyen Tashar Bama, da Dogun Muazu da kuma Unguwar Maigayya dake karamar hukumar sabuwa dake jihar katsina.

Ko a karanar hukumar faskari ta jihar Katsina yan bindiga sun kashe wani manomi yana cikin aikin gonar mahaifinsa inda kuma suka yi awon gaba da sauran yan uwansa biyu da suke aiki tare a cikin gonar.

Sannan ko a ranar asabar wani manomi daga yankin karamar hukumar Sabuwar ya tabbatar wa Katsina Daily Post News cewa mahara sun tare hanyar shiga wasu kauyuka a Sabuwar domin hana fita a ci kasuwar Dandume, inda suka yi kira da murya mai karfi zuwa ga gwamnatin jihar Katsina ta kai masu daukin gaggawa kan lamarin.

Kisan gillar na zuwa ne kasa da awanni 24 da yi wa mutum 43 zana’ida a jihar Borno sakamakon yankan ragon da yan Boko Haram suka yi masu suna cikin aikin shinkafa a gonakinsu

Related posts

Leave a Comment