Ministan matasa da ci gaban Wasanni, Mista Sunday Dare, ya ce zasu iya kashe a kalla nera Miliyan N81 wajen nome Ciyawar Filin wasanni na kasa na MKO Abiola National stadium, dake babban birnin tarayya Abuja.
Filin wasannin mai fadin Hekta 29, Wanda aka gina Lokacin Shugaba Obasanjo, a shekarar 2003, wanda ya lakume nera Biliyan 53.
Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da Jawabin sa a wani taron karawa Juna Sani na kwana guda da kungiyar masu rubuce-rubuce a fagen wasanni SWAN suka shirya a babban birnin tarayya Abuja.
Majiyar mu ta Daily-Trust ta bayyana mana cewar Ministan ya ce suna bukatar makudan kudaden ne biyo bayan wata kididdiga da hukumar kula da tsaftar mahalli AEPB ta fitar.
A kan haka Yan Najeriya zasu fara gutsiri tsoma kan cewa Nome Ciyawa zata iya lakume nera miliyan 81, to ai babu ma kudaden a kasa, hakan ya saka zamu hada hannu da masu hannu da shuni don ganin abubuwan sun gudana yadda ya kamata; inji Ministan
