Tsohon Sanata da ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattawa Kwamared Shehu Sani, ya soki hukumar Hisbah ta jihar Kano kan gargadin da ta yiwa wani gidan rediyo na amfani da kalman ‘Black Friday.’
Shehu Sani a shafinsa na Tuwita ya ce wannan rashin aikin yi ne kuma yayi kira ga Hisbah ta mayar da hankalinta kan garkuwa da mutane da kashe-kashen da ake yi a Arewa, ba surutu mara amfani ba.
“Ranar Juma’a babbar rana ce ga Musulmai. Dan an ambaceta da wani kala ba wani abu bane. Barazanar Hisbah kan amfani da kalmar ‘Black Friday’ aikin banza ne,” cewar Shehu Sani.
“Su mayar da hankali kan kashe-kashe da sace-sacen mutane a garinsu. Ana bukatansu a filin daga,”.
Tun bayan sanarwar da Hisbah ta yi na haramta amfani da wannan kalma ta Black Friday, ake ta samun sauye sauyen ra’ayoyin jama’a akai, wasu na yabo wasu na suka.
