Babban malamin addinin islama Sheikh Abdullahi Gadon Kaya ya bayyana cewa rashin adalcin Shuwagabanni na daya daga cikin abinda ya kawo rashin Tsaro a arewacin kasar nan.
Malamin ya bayyana hakan ne yayin zantawa da wakilin jaridar muryar yanci a Kaduna inda ya bayar da misalai da dama kamar haka:
Muddin gwamnati da Shugabanni ba zasu dinga adalci ga kowa ba dole ne ayyukan ta’addanci suyi kamari a kasar nan. Babu yadda za a ware wasu mutane daban ace su kadai ne gwamnati zata dinga tallafa masu ko kuma wasu mutane kalilan ace su kadai ne zasu dinga anfana da tallafin gwamnati.
Baza ace gwamnati bata bada tallafi ba amma koda ta bayar baya zuwa wurin Wanda suke tsananin bukata.
Maganar kyale manyan dillalan masu miyagun kwaya suna yawo ba tare da hukunci ba shima ya kara taka muhimmiyar rawa wurin samun matsalar rashin tsaro. Babu yadda za ace wai gwamnati bata san yadda ake safarar miyagun Kwaya a fadin kasar nan ba. Kuma wallahi idan aka kawo karshen hakan za a samu saukin tsaro a kasar nan.
Idan Shuwagabanni basa son matsalolin tsaron nan su shafe su, ya zama wajibi su dinga yiwa kowa adalci suma a kan kunerunsu
Daga karshe babban malamin yayi kira na musamman ga daukacin al’umma da su sani cewa idan har ana son kawo karshen matsalar nan sai kowa ya sauya munanan halayyar da yasan yanayi mara kyau. A nemi afuwar Allah kowa yayi gyara a inda yake sannan komai zai daidaita insha Allahu.
