Tattalin Arziki: Gwamnatin Neja Za Ta Zaftare Albashin Ma’aikata

Gwamnatin Jihar Neja ?ar?ashin jagorancin Gwamnan jihar Abubakar Sani Bello ta kammala shirye-shirye don yanke albashin ma’aikata a jihar da kaso 50 cikin dari domin rage ra?a?in matsalar tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta.

Gwamnatin jihar ta fada ma manyan jami’ai na kungiyar kwadago a wani taro a ranar Litinin, 25 ga watan Nuwamba, cewa ba za ta iya ci gaba da biyan kaso 100 na albashin ma’aikata ba daga watan Disamban 2020.

An tattaro cewa taron ya samu halartan dukkanin mambobin majalisar zartarwa ta jihar illa Gwamna Alhaji Abubakar Bello da mataimakinsa Alhaji Ahmed Mohammed Ketso.

Babban akawu na jihar, Alhaji Abdullahi Saidu ne ya sanarwa da shugabannin kungiyar kwadago halin da ake ciki na dalilin shirin yanke albashin.

An tattaro cewa babban akawun ya yi bayanin cewa akwai ragowa sosai a kudaden da jihar ke samu daga asusun gwamnatin tarayya da kudaden shiga. Sai dai, gwamnatin jihar ta yi alkawarin biyan ma’aikata kaso 50 da aka yi masu ragi da zaran tattalin arziki ya inganta.

Shugabannin kungiyar kwadago sun yi martani akan wannan mataki na gwamnatin Jihar inda suka sha alwashin nuna turjiya a kan shirin yanke albashin ma’aikatan.
Basu amince da bayanin gwamnatin jihar da alkawarin biyan ragin da aka yi daga albashin daga baya ba.

Related posts

Leave a Comment