?an Majalisar Dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisa Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewar zai ?aukaka ?ara sakamakon cin zarafin da aka yi mishi ta hanyar kamu da jefa shi Kurkuku da Gandirebobin Kurkukun Kuje a birnin tarayya Abuja suka yi jiya Litinin.
Lauyan Sanata Ndume, Barista Marcel Oru, ya ce za su daukaka karar ne yau talata a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja, domin tabbatar da ganin adalci ya tabbata akan ?an Majalisar.
Lauya Marcel Oru yace ba a ba Ndume damar jin ta bakinsa ba, sannan ba su bashi wasu takardu da ya bukata ba don ya kare kansa, kawai an yi amfani da wata dama ne domin aci mutuncin sa.
“Muna bukatar wasu takardu don gabatar da ita gaban alkali don kare Ndume,” cewar lauyansa. “Ba a yi mana adalci an bamu wannan damar ba, kafin kotu ta zartar da hukunci,” cewarsa.
Wata majiya ta kusa da Ndume, ta ce an tafi dashi gidan Kurkuku da misalin karfe 4 na yammacin jiya.
Ya ce wayoyinsa ba sa tafiya, duk a kashe, tun bayan da kotu ta bayar da umarnin tafiya dashi gidan Yarin.
“Za a koma da Ndume kotu yau don cigaba da shari’ar. Tunda kotu ta bayar da zabi 3, kuma muna fatan zai cika ko da zabi daya ne don su sake shi,” kamar yadda majiyar tace.
