Masu garkuwa da mutane sun sa kudin fansa a kan ?aliban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, da aka sace a kan hanyar zuwa birnin tarayya Abuja a makon da ya gabata.
‘Yan Bindigar sun nemi a biya Naira miliyan 270 kafin su fito da wadannan ?alibai har tara da su ka tsare, ko kuma labari ya sauya.
Wani daga cikin wadanda ‘yan bindigan su ka tsare, Dickson Oko, ya yi nasarar kubuta, ya kuma shaida wa manema labarai halin da ake ciki.
Dickson Oko ya ce miyagun sun tuntubi ‘yanuwan ?aliban da su ka tsare inda su ka bukaci kowanensu ya biya miliyan 30 a matsayin fansa.
Oko wanda ya aka yi wa rauni da bindiga a dalilin harin ya na samun sauki a yanzu, amma hankalinsa a tashe ya ke saboda tsare takwarorinsa.
Matashin ya shaida wa manema labarai cewa ya na cikin wadanda su ka tsere a lokacin da ‘yan bindigan su ka tare su a kan hanyar su ta zuwa garin Abuja. Mista Oko ya ce shi da direbansu mai suna Nuruddeen Mohammed sun ci kafar kare, inda har ya bar wayoyin salularsa da wasu kaya a cikin motarsu.
Mutane 12 ne a wannan mota da ta dauko yaran makarantar, daga ciki an kama mutum tara. Iyalan wata mace daga cikin ‘daliban sun fada wa VOA Hausa cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntube su, kuma sun bukaci miliyan 30 daga gare su.
