Manyan Malaman Kirista 42 Da Iyalansu Sun Kar?i Musulunci A Abuja

Rahotanni daga Abuja sun bayyana cewa addinin musulunci ya samu ?aruwa da wasu manyan Pastoci 42 tare da matan su da wasu manyan Bishop biyu da iyalansu sai wata babbar Pasto ?aya Mace da Sista guda.

Bayin Allahn inda sun karbi musulunci a babban ?akin taron na Babban Masallacin ?asa dake babban birnin tarayya Abuja.

Bisa bayanai da majiyar mu ta Zuma Times ta samu, an shirya musu taro na musamman domin ilmantar da su har na kwanaki bakwai a dakin taro na babban masallacin dake Abuja.

Musuluntar tasu dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen yammacin duniya ke cigaba da sukar lamirin musulunci da arsasa farfagandar kyamatar addinin a zu?atan jama’a dake rayuwa a ?asashe masu tasowa.

Muna addu’ar Allah tabbatar da imanin su akan tsayuwa bisa addinin da kuma kare su daga dukkanin wani sharri na magauta Allahumma Amin.

Related posts

Leave a Comment