Zamfara: An Ceto ‘Yan Mata 26 Daga Hannun ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga Jihar Zamfara sun tabbatar da cewar jami’an tsaro sun yi nasarar ceto wasu ‘yan Mata har su 26 da’yan Bindiga suka yi garkuwa da su a jihar.

Da yake zantawa da manema labarai a Gusau babban birnin Jihar, mai magana da yawun gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawallen Maradun, wato Zailani Baffa ya bayyana cewar dukkanin ‘yan matan su 26 an sato su ne daga yankin ?aramar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina a kwanakin baya.

Baffa ya ?ara da cewar a halin yanzu tuni an mayar da ‘yan Matan gaban iyayensu a Jihar Katsina.

Lamarin sata gami da garkuwa da mutane dai ya zama ruwan dare a yankin arewa maso yammacin kasar musanman a Jihohin Zamfara da Katsina, inda jama’a da dama suka ?auracewa gidaje da gonakin su saboda fargabar ‘yan Bindiga.

Related posts

Leave a Comment