Rahotanni daga ?asar Saudiyya sun bayyana cewa wata mota ta sanya kai gadan-gadan cikin Masallacin Ka’aba a guje, har ta kai ga gab da kofar shiga cikin masallacin na Harami.
Kakakin gwamnan Makka, Sultan al-Dosari, ya ce lamarin ya afku ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar Juma’a, 30 ga watan Oktoba, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Saudiyya (SPA) ya ruwaito.
An tattaro cewa motar ta kutsa kai cikin farfajiyar ?ofar Sarki Fahd, wanda aka hade da masallacin ta baya.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda motar ta yi awon gaba da ababen kariya sannan ta dangana ga kofar shiga masallacin.
Kamar yadda sashin Hausa na BBC ya ruwaito , majiyoyi da dama sun jaddada cewa motar ta shiga farfajiyar masallacin ne ta kan Titi na 15, wanda ita ce babbar hanyar da ta dangane da cikin Farfajiyar Sarki Fahd da ke Masallacin Harami.
An kuma tattaro cewa babu ko mutum guda da ya jikkata a hatsarin yayinda aka damke direban a nan take. An kuma daure hannayensa kafin aka tisa keyarsa.
“Motar ta dangana ga kofar ne yayin da ta kwaso mugun gudu a kan daya da cikin titunan da ke kusa da farfajiyar masallacin ta bangaren kudu. Amma kuma babu wanda ya jikkata,” in ji Sultan al-Dosari.
Ya ci gaba da fadin cewa: “An cafke direban. Dan Saudiyya ne kuma ba ya cikin hankalinsa. An mika shi wurin masu shigar da kara.”
Shingen da ake sakawa a bakin kofar masallacin ba masu kwari ba ne, abin da ya sa motar ta wancakalar da su kenan, kamar yadda ake iya gani a bidiyon da aka watsa.
Shafin Haramain Sharifain ya ce nisan da ke tsakanin ?ofar da motar ta shiga zuwa cikin masallacin bai fi mita 230 ba.
