Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Gui?i

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Asabar, goma sha hudu ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da talatin da daya ga watan Oktoba, shekarar 2020.

  1. Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya Mohammed Adamu, ya ce babu gaskiya a zargin da kungiyar kare hakkin bil’Adama ta Aminasti ta yi cewa jami’an tsaro sun yi amfani da karfin tuwo har da kisa ga masu zanga-zangar lumana ta #ENDSARS. Ya ce ‘yan sanda ne ma masu zanga-zangar suka kashe, suka ji wa da dama rauni, suka banka wa ofisoshin ‘yan sanda masu yawan gaske wuta. Ya ce dan sanda ma fa mutum ne abin tausayawa.
    Ya ma leka sansanin ‘yan bautar kasa da sauran wurare da ke Abuja da masu zanga-zangar suka yi wasoson kaya.
  2. Majalisar Dinkin Duniya ta karrama ‘yar sandar Nijeriya, a matsayin ‘yar sanda gwarzuwa da ta ciri tuta a aikin wanzar da zaman lafiya na majalisar.
  3. Shekaranjiya Alhamis ‘yan bindiga sun leka jihar Zamfara suka tafka barna ba ‘yar kadan ba.
  4. Jiya da daddare ‘yan fashi sun tare tsakanin hanyar Zariya da Kano.
  5. Iyayen yara da ke karatu a jami’a a Nijeriya na ci gaba da korafin yara sun gaji da zaman gida, saboda yajin aikin malaman jami’a da alamu ke nuna da sauran zama a gida. Ba ranar komawa makaranta.
  6. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 170 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 106
Abuja 25
Oyo 14
Edo 7
Kaduna 7
Ogun 4
Bauci 2
Binuwai 2
Kano 1
Oshun 1
Ribas 1

Jimillar da suka harbu 62,691
Jimillar da suka warke 58,430
Jimillar da ke jinya 3,117
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,144

  1. Gwamnatin Tarayya za ta soma rabon mitar wutar lantarki ga mutum miliyan talatin kyauta.
  2. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, sun yi korafin ana mayar da ma’aikatansu da suka shiga tsarin IPPIS ‘yan bora wajen biyan albashi idan wata ya kare, har ma da ariyas da suka doshi shekara biyu suna bi na sabon albashi. Suka yi korafin tun litinin aka soma biyan sauran ma’aikatu, su kuwa idan ba a yi sa’a ba sai kusan tsakiyar watan gobe. Suka ce haka ma ariyas, sauran ma’aikata sun fi shekara da aka biya su, amma su sun doshi shekara biyu duk da sun shiga IPPIS an ki biyansu.
  3. Kungiyar Malaman jami’a ASUU, ta zargi gwamnatin tarayya da rashi ajiye magana. Ta yi zargin sai sun kulla alkawari da gwamnati kamar da gaske, sai lokaci ya zo gwamnati ta saba alkawarin.
  4. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  5. Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka CAF Ahmad, ya harbu da kwarona.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Gaisuwa ta musamman ga Farfesa Ramlat Jibir-Daura da Farfesa Sadiq Mohammed dukkansu malamai a Tsangayar Ilimi,, ta Jami’ar Ahmadu Bello, Samarun Zariya.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Related posts

Leave a Comment