Zanga-Zangar #EndSARS: Ku Guji Saurin Yanke Hukunci : Buhari Ga Kasashen Duniya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi kasashen duniya da su guji saurin yanke hukunci kan batun da ya shafi zanga-zangar EndSARS.

Buhari wanda ya bayyana haka a ranar Alhamis, ya gode wa kasashe makwabta da sauran ?asashen duniya kan damuwar da suka nuna ga abunda ke faruwa a Nijeriya, saidai ya yi kira a gare su da a ko yaushe su ri?a tabbatar da zance kafin daukar matsaya ko saurin yanke hukunci.

Tun da farko dai kungiyar Tarayyar Turai EU da Amirka da kuma sauran kasashe da kungiyoyin duniya sun yi tir da harin da aka ce an kai wa masu zanga-zangar.

A wata sanarwa da Amirka ta fitar ranar Alhamis ta yi kira ga hukumomin tsaro su nuna ?warewa tare da girmama yancin masu zanga-zangar.

Ita ma EU cewa ta yi ta ka?u da samun labarin kisan da aka ce an yi wa masu zanga-zangar.

Ku kasance da shafin mu na www.muryaryanci.com domin samun ingantattun labarai a koda yaushe

Related posts

Leave a Comment