Ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige, yace gwamnati bata da halin samarwa matasa marasa ayyukan yi da suke yawo kwararo-kwararo a titi ayyukan gwamnati, saboda haka idan dama ta ?iyi, sai a koma hagu.
Ngige ya roki ma’aikatu masu zaman kansu da su taimaka su samar wa marasa ayyukan yi wuraren da zasu rabe don kawo karshen rashin ayyuka a kasar nan.
Ministan ya bayyana hakan ne a yayin bude taron samar da ayyukan yi mai “Samar Da Cigaban Ma’aikatu Masu Zaman Kansu” wanda ya gudana ranar Litinin a birnin tarayya Abuja.
Sakataren ma’aikatar, Yerima Peter Tarfa ne ya wakilci ministan, ministan ya ce wani nauyi ne akan gwamnati ta samar da wurare don taimakon ma’aikatu masu zaman kansu su samar wa marasa aiki gurbi.
Ministan ya nemi jin ta bakin wadanda suka je taron don samun shawarwari akan yadda za’a bullo wa lamarin.
Rashin ayyukan yi a Najeriya musamman tsakanin Matasa na cigaba da zama wata barazana ga ?asar, inda matasa da dama da suka kammala karatu a manyan makarantu ke cigaba da gararanba a tituna domin neman abin yi.
