Ministan Ya?a Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ne ya bayyana haka, lokacin da yake wa manema labarai ?arin bayani a Fadar Shugaban ?asa, bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa a ranar Laraba.
Ya ce majalisar zartarwa ta yanke shawarar jingine ayyukan kwangilolin Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, wa?anda gwamnatin Tinubu ta gada, masamman wa?anda ke bu?atar sai an ?ara narka masu ma?udan ku?a?e.
Ya ce Shugaba Tinubu ya ce wannan takardar shawarar da Ministan Ayyuka, Davida Umahi ya gabatar wa Majalisar Zartaswa, ya na so a binciki kwangilolin kuma a sake tattauna batun su a taron Majalisar Zartaswa na gaba.
Idris ya ce za a yi bin-diddigin ne domin sake nazarin ayyukan da ke bu?atar ?arin ku?i da wa?anda ke bu?atar duba shi kacokan.
Minista Idris ya ce Tinubu ya umarci Ministan Ayyuka ya yi aiki tare da Ministan Kasafin Ku?i da Tsare-tsare da Ministan Harkokin Ku?a?e su sake nazarin ayyukan kwangilolin, domin gabatar da su a bisa tsarin ?e?e-da-?e?e, wanda ke bisa turbar ?a’idojin da ke cikin dokokin kasafin ku?i.
Ministan ya ?ara da cewa, “duk inda ke bu?atar tilas sai an ?ara ku?i, to za a gabatar da batun sa a taron Majalisar Zartaswa na gaba, domin a sake tattaunawa akai.
Idris ya ce Majalisar Zartaswa ta kuma tattauna dangane da Majalisar Tantance Kwangiloli (National Procurement Council), wadda kusan tsawon shekaru 17 kenan ta daina yin wani tasiri.
A kan haka ya ce Shugaban ?asa ya aika da ?udiri a Majalisa, wanda tuni har an yi masa karatun farko.
“Ma?asudin yin haka shi ne domin mu tabbatar da Majalisar Tantance Kwangiloli mai tasiri, karsashi wadda za ta ri?a duba da nazarin kowace kwangila, domin tabbatar da sahihancin adadin ku?a?en da za a kashe mata,” inji ministan.
