Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da karar da ke neman soke mu?amin da shugaba Bola Tinubu ya bai wa Hannatu Musawa a matsayin ministar fasaha da al’adu da tattalin arziki.
Mai shari’a James Omotosho, a cikin wani hukunci, ya ce wadanda suka shigar da karar ba su da hurumin yin karar.
Mai shari’a Omotosho ya kuma bayyana cewa ko a inda aka baiwa masu karar damar shigar da karar, ita kanta karar ba ta kamata a shigar da ita ba.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, a ranar 27 ga Yuli, 2023, Shugaba Tinubu ya mika sunan Musawa, cikin sunayen wadanda aka nada a matsayin ministoci, ga majalisar dattawa don tabbatarwa.
Musawa, wacce lauya ce, ta samu tantancewa daga majalisar dattawa a ranar 1 ga Agusta, 2023, kuma aka rantsar da ita a matsayin minista a ranar 21 ga Agusta, 2023.
Kamar yadda a lokacin da aka nada ministar wadda ‘yar asalin jihar Katsina ce, an ce ta kasance tana bautar kasa (NYSC).
Dangane da wannan batu, shine wasu mutane biyu, shugaban ‘Incorporated Trustees of Concerned Nigeria’, Cif Dr Patrick Eholor da Thomas Marcus, wadanda su ne masu kara na 1 zuwa na 3, su ka shigar da kara a gaban mai shari’a Omotosho, suna masu kira da a sauke ta saboda an sa?awa doka.
