Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa rundunar ‘yan sanda an birnin sun ritsa wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne a ma?oyarsu cikin dazuka da tsaunuka da ke kewayen Apo.
Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
Sanarwar ta bayyana cewa “jami’an rundunar ?ar?ashin jagorancin kwamishinan ?an sanda CP Benneth Igweh sun kai samame cikin dazuka da ke kewayen shiyyar Zone A da B na unguwar Apo domin tabbatar da matakan tsaro a yankin saboda ana ganin wurin ya zama ma?oyar masu sace mutane.
“Sumamen ya ha?a da ?one gidajen da aka yi ba bisa ?a’ida ba da dazukan da ke kewayen tsaunuka da kuma tura ?an sanda su yi rangadi a yankunan.
A cewar sanarwar, Igweh ya umarci mutane su ci gaba da taka tsan-tsan sannan su kai rahoton duk abin da zuciyarsu ba ta yi na’am da shi ba ga ?an sanda.
