Majalisar Tarayya ta sha alwashin cewa sai ta ?wato jiragen sama biyu ?irar Bell 206L4 BZB da kuma Bell M2062-L4, wa?anda mallakar Kwalejin Koyon Tu?in Jirage ne (NCAT) da ke Zariya, amma aka sayar da su ga wasu shafaffu da mai.
Shugaban Kwamitin Bin Diddigin Kadarorin Gwamnati, Ademoyin Kuye ne ya bayyana haka, a lokacin zaman binciken da kwamitin ya yi, inda ya saurari bayanin yadda aka sayar da jiragen biyu.
An yi zaman kwamitin sauraren sabar?alar a Majalisar Tarayya, ranar Alhamis, a Abuja.
Kuye ya bayyana cewa abin damuwa ne matu?a jin yadda aka sayar da jiragen ga wasu mutane, lamarin da ya sa kwalejin ta kasance ba ta da sauran jiragen koyon tu?i ko ?aya.
Haka kuma kwamitin ya tambayi yadda aka yi har aka sayar da jiragen biyu ga wasu mutane daban, alhali kuma Rundunar Sojojin Saman Najeriya, Rundunar Sojojin Ruwa da kuma Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya duk sun nuna bu?atar saye, amma aka ?i sayar masu, aka saida wa wasu mutum biyu daban.
Binciken ya nuna cewa mahukuntan kwalejin ne suka ?i sayar wa jami’an tsaro jiragen.
Majalisar Tarayya ta gano cewa ?angarorin jami’an tsaro ukun da suka rubuta takardar neman a sayar masu da jiragen, sun kuwa tura tawaga har cikin kwalejin domin gane wa idanun su yadda jiragen suke, amma duk da haka aka ?i sayar wa wasu daban.
Shugaban Ri?o na Kwalejin Koyon Tu?in Jirage da ke Zariya (NCAT), Shakespeare Imalighwe, ya ce duk da a lokacin da aka sayar da jiragen ya na Mataimakin Shugaba, ba a yi shawara da shi ba wajen sayarwar, ?arshe ba a ma saka shi cikin ‘yan kwamitin sayar da jiragen ba.
Ya ce ya kar?i kwalejin a matsayin Shugaban Ri?o cikin Janairu, 2024.
Ya shaida wa kwamitin cewa jiragen lafiya ?alau suke a lokacin da aka sayar da su. Kuma a a lokacin akwai kamfanin da ke kula wajen yi wa jiragen garambawul kafin a sayar da su.
Daga nan ya shaida masu cewa a zaman yanzu dai babu jirgin koyon tu?i a kwalejin ko ?aya.
Daga nan kwamiti ya umarci tsohon Ministan Sufuri Hadi Sirika da Ministan Sufurin Jiragen Sama na yanzu, Festus Keyamo su bayyana gaban kwamitin.
