‘Yan Bindiga Na Cigaba Da Daukar Rayuka A Jihar Neja

IMG 20240323 WA0041

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewa wasu ?an bindiga sun halaka mutum 21 ciki har da magajin gari a kauyen Madaka da ke ?aramar hukumar Rafi a jihar Neja. Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Premium Times cewa ?an bindigan sun yi awon gaba da adadi mai yawa na mutane, wa?anda har yanzu ba a tantance yawansu ba.

A cewar majiyoyin, ‘yan bindigar sun kuma kona gidaje da shaguna kusan 50, da kuma motoci da babura da dama yayin wannan mummunan harin. Yadda ?an bindiga suka yi ?arna Sun ce ‘yan bindigar dauke da muggan makamai sun shiga kauyen kana suka bu?e wuta kan mai uwa da wabi, kafin daga bisani su fara kashe-kashe da ?one-?one. Wani mazaunin kauyen ya ce saboda babu jami’an tsaro kauyen shiyasa ?an bindigan suke shiga su yi abin da ransu ya so babu mai ?aga masu yatsa. Hakimin yankin, Isah Bawale, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar a Minna, babban birnin jihar, a wata tattaunawa ta wayar tarho.

An tattaro cewa shekara ?aya da ya gabata, ?an bindiga sun kai farmaki wannan kauyen kuma sun kashe magajin garin.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya ce yana ci gaba da kokarin tantance rahotannin abin da ya faru a harin. Kwamishinan tsaro na jihar, Bello Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce gwamnati na kokarin tsare dukkan garuruwan da ke noma a jihar.

Related posts

Leave a Comment