Matsalar Tsaro: Addu’a Ce Mafita – Sanata Marafa

IMG 20240321 WA0068

Tsohon Sanata a jihar Zamfara, Kabiru Marafa ya bayyana hanyar dakile matsalar tsaro da ta addabi Najeriya. Sanata Marafa ya ce hanya daya mafi sauki domin dakile matsalar ita ce addu’a da kuma hadin kai daga ‘yan kasar.

Ya ce wannan hadin kai da addu’a ana bukatarsu ne daga dukkan ‘yan kasar ba tare da bambancin addini ko kabilanci ba.

Marafa wanda ya wakilci mazabar Zamfara ta Tsakiya daga shekarar 2011 zuwa 2019 ya bayyana haka a ranar Talata 19 ga watan Maris. Ya ce matsalar tsaron za ta kawo karshe idan har ‘yan kasar suka hada kai ba tare da nuna bambanci a tsakani ba.

Ya kuma bukaci al’ummar Musulmai da su yi amfani da wannan watan Azumi domin yin addu’a ga ci gaban kasar.

“A yayin da mu ke fama da matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki, ya kamata mu hada kai domin kawo karshen matsalolin.”

“Ba tare da bambancin addini ba, yanzu lokaci ne da ya kamata mu hada kai tare da yin addu’o’i domin ci gaban kasar.”

“A wannan wata na Ramadan, ya kamata mu kara kaimi wurin yin addu’a domin samun kwanciyar hankali da kuma ci gaban Najeriya.”

Related posts

Leave a Comment