Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga ?aukacin shugabannin Afirka da su tashi tsaye wajen dakile aukuwar juyin mulkin sojin domin tabbatar da wanzuwar dimokura?iyya.
Tinubu ya bukaci takwarorin nasa da su mutunta ’yancin dimokura?iyya da doka-da-oda da kuma wanzuwar siyasa musamman a wannan lokaci da ake fuskantar kalubale kama daga annobar Coronavirus da matsalar tsaro da dumamar yanayi.
Shugaba Tinubu ya yi wannan kira ne a taron tsakiyar shekara na gamayyar Kungiyoyin Ha?in Kan Afirka da na rassan ?ungiyoyin tattalin arzikin ?asashen yankin Afirka da ke gudana a Nairobi, babban birnin ?asar Kenya.
A cikin kunshin bayanan da Babban Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Adamu Ibrahim Lamuwa ya gabatar, Tinubu ya bu?aci mahukuntan ?asashen na Afirka da su tabbatar sun mutunta batun sake sabunta mulkin dimokura?iyya.
Shugaban Najeriyar wanda ya kasance sabon shugaban kungiyar ECOWAS, ya ce ya kamata a yi watsi da batun juyin mulki a fa?in nahiyar, musamman ma wannan lokaci da ake fama da rashin tsaro da sauyin yanayi da kuma annobar korona.
Ya ce abin takaici ne ganin cewa duk da kasancewar Yammacin Afirka sahun gaba wajen ?abbaka dimokura?iyya da kuma kyakkyawar shugabanci, ita ke gaba a yankin wajen amfani da hanyoyi da suka sa?a wa kundin tsarin mulki don sauya gwamnati.
Ya kuma yi garga?in cewa yawaitar kifar da gwamnatoci da ake samu a Afirka, na barazanar kawo rashin zaman lafiya da tsaro, da janyo talauci da ?ai?aita mutane wajen raba su da muhallansu.
“Tsakanin 2020 zuwa yanzu, Afirka ta fuskanci juyin mulki guda shida da kuma guda uku wanda ba a samu nasara ba. Hakan na janyo tarnaki ga tsarin dimokura?iyyar mu a Afirka.
“Don haka, na ke kira ga ?aukacin shugabannin Afrika da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun mutunta ?ancin dimokura?iyya da kuma doka-da-oda don tabbatar da ?orewar siyasa a nahiyar,” in ji Tinubu
