Atiku Ya Halarci Rantsar Da Gwamna Fintiri Na Adamawa

?an takarar adawa na jam’iyyar PDP a Najeriya, Atiku Abubakar, ya halarci bikin rantsar da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin gwamnan Adamawa.

Da safiyar ranar Litinin aka rantsar da Fintiri don jagorancin jihar, wadda ita ce mahaifar Atiku, karo na biyu bayan ya yi nasara a ?ar?ashin jam’iyyar PDP.

“Na bi sawun al’ummar Jihar Adamawa wajen taya Gwamna Fintiri da mataimakiyarsa Farfesa Kaletapwa Farauta murnar nasara da kuma rantsuwar kama aiki a karo na biyu,” in ji Atiku cikin wani sa?on Twitter.

A yau Talata kotun sauraron ?ararrakin za?e za ta ci gaba da zama a shari’ar ?alubalantar nasarar Bola Tinubu, wadda Atiku da PDP suka shigar duk da cewa an rantsar da shi a yau.

Related posts

Leave a Comment