Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma shugaban kasa Muhammdu Buhari ya umarci ministocinsa su ci gaba da aiki har zuwa jajiberin ranar sauka daga mulki.
An yi ta hasashen shugaban zai rushe majalisar ministocin tasa a yau Laraba yayin zaman ?arshe da ya jagoranta bayan shafe shekara takwas a kan mulki.
Sai dai shugaban ya umarce su da su ci gaba da aiki har zuwa ranar Lahadi, 28 ga watan Mayu, kamar yadda Ministan Ya?a Labarai Lai Mohammed ya bayyana wa manema labarai.
A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu za a rantsar da shugaba mai jiran gado Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya na 16.
An gudanar da zaman ne a ?akin taro na fadar shugaban ?asa da ke Abuja.
Mahalarta taron sun ?unshi Mataimakin Shugaban ?asa Yemi Osinbajo da dukkanin ministoci 44 na gwamnati da kuma ?ananan ministoci.
An gabatar da jawabai na yadda al’amura suka kasance tsawon mulkin shugaban ?asar da kuma jawaban ban-kwana.
A ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015 ne Muhammadu Buhari ya hau kan mulki bayan doke tsohon shugaban ?asa mai ci Goodluck Jonathan.
A lokacin da ya hau mulki, Buhari ya yi al?awarin mur?ushe rashin tsaro ta hanyar kawar da ?ungiyar Boko Haram, da ya?i da rashawa da kuma ya?i da talauci.
