Kungiyar dake rajin ya?i da cin hanci da rashawa dake zamanta a Kaduna ta yi kira ga hukumomi da su yi gaggawar yin sakayya ga jami’in ?an Sandan da ya ki kar?ar cin hanci na Naira miliyan 50 daga wasu ‘yan kasar China.
Jami’in ‘yan sandan mai suna Abdullahi Lawal wanda tsohon jami’i ne na hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa EFCC Shiyyar jihar Sokoto, ?ungiyar ta bayyana shi a matsayin barde mai gaskiya kuma abin koyi.
Shugaban kungiyar Kwamared Shehu Abubakar ya sanar da hakan a yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Kaduna jim ka?an bayan da kotun ?aukaka ?ara ta Kaduna ta bada Umarnin ingiza ?eyar ‘yan kasar Chinan biyu zuwa gidan yari.
Abubakar ya yi kira ga hukumar dake kula da ayyukan ‘yan sanda da cewar cikin gaggawa ta yi aikin sakayya ga gwarzon jami’in ‘yan sandan domin zama darasi ga ‘yan baya.
Kotun daukaka ?arar ta samu ‘yan ?asar Chinan biyu Mr. Meng Wei Kung da Mr. Xu Kuai da laifin cin amanar kasa da damfara da kuma yunkurin bayar da cin hancin Miliyan 50 ga ‘yan sandan.
“Muna kira ga hukumomin da abin ya shafa su yi ?arin girma ga Abdullahi Lawal da sakayya mai kyau, domin hakan zai taimaka gaya wajen karfafa gwiwa ga sauran ‘yan sandan wajen ya?i da cin hanci da rashawa a fa?in ?asar nan.
